'Yan wasan Chelsea sun ba marada kunya

Image caption Chelsea tana mataki na 15 a kan teburin Premier

Jose Mourinho ya ce 'yan wasansa sun kunyata masu sukar kokarin da suke yi, duk da fitar da su da aka yi daga gasar Capital One Cup a ranar Talata.

Chelsea ta yi rashin nasara ne a hannun Stoke City da ci 5-4 a bugun fanariti, bayan da suka tashi wasa kunnen doki a minti 120 da suka yi.

Kocin ya ce 'yan wasan sun kalubalanci masu kushesu, suka kuma ba su kunya a fafatawar da suka yi a filin Britannia.

Mourinho ya ce abin takaici ne ace 'yan wasa ba sa saka kaimi, domin sun yi iya kokarinsu domin su lashe wasan.

Chelsea wacce ke mataki na 15 a kan teburin Premier, an cire ta daga Capital One Cup wanda ta dauka a bara.