Giwa FC ta doke Wikki Tourists da ci 3-2

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption Saura wasanni uku kenan a kammala gasar Firimiyar Nigeria ta bana

Giwa FC da ci Wikki Tourists 3-2 a gasar Firimiyar Nigeria wasannin mako na 35 da suka buga a ranar Laraba.

Wikki ce ta fara cin kwallo a minti na 10 da fara tamaula ta hannun Idris Sabo, a inda Giwa FC ta farke kwallon ta hannun Saleh Mohammed a minti na 23.

Harrison Madu ne ya kara ci wa Wikki kwallo ta biyu a raga a minti na 38, kuma Amos Gyang ya farkewa Giwa FC saura minti uku aje hutun rabin lokaci.

Daf da za a tashi wasa ne Giwa FC ta zura kwallo ta uku a ragar Wikki ta hannun Amos Gyang.

Karawa tsakanin Taraba FC da Nasarawa United ta gamu da cikas bayan da 'yan kallo suka shiga filin wasa.

Ga sakamakon wasannin mako na 35 da aka buga:

  • Dolphins 2-0 El-Kanemi
  • FC Ifeanyiubah 1-0 Heartland
  • Sharks 2-1 Shooting Stars
  • Enyimba 1-0 Kwara Utd
  • Bayelsa Utd 1-0 Abia Warriors
  • Akwa Utd 2-1 Sunshine Stars
  • Kano Pillars 2-1 Rangers