Capital One Cup: Southampton da Liverpool

Image caption Kociyan Liverpool Yurgen Klopp

Southampton za ta kece raini da Liverpool a wasan daf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin Capital One.

Middlesbrough kuwa, wacce ta fitar da Manchester United daga gasar a bugun fenariti, za ta fafata ne da Everton.

Ita kuwa Manchester City, wacce ke buga gasar Zakarun Turai a Ettihad za ta karbi bakuncin Hull City.

Stoke City kuma, wacce ta yi waje da Chelsea daga gasar, za ta yi gumurzu ne da Sheffield Wednesday wacce ta fitar da Arsenal.

Za a fara buga wasannin daf da na kusa da na karshe a Gasar Capital One din a ranar 30 ga watan Nuwamba.

Ga jadawalin wasannin da za a yi:

Middlesbrough v Everton

Southampton v Liverpool

Stoke City v Sheffield Wednesday

Manchester City v Hull City