"Sa'a kawai Middlesbrough suka yi suka ci Man-U"

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Sa'a Middlesbrough suka yi suka ci Man-U, in ji Koci Louis Van Gaal

Kociyan kungiyar Manchester United, Louis van Gaal, ya ce ci dayan da Middlebrough ta yi wa kungiyarsa, sa'a ce kawai.

Kungiyar Middlebrough dai ta doke Manchester United da ci uku da daya a bugun feneriti bayan da aka shafe mintuna 120 na wasan ba ci a Old Trafford.

Van Gaal ya ce "Ko a jiya mun yi atisaye a kan bugun fenariti, amma duk da haka sun samu sa'a a kanmu.

Wannan dai shi ne karo na hudu da aka ci Manchester United a bugun fenariti.