Watakila Mourinho ya jagoranci wasa da Liverpool

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Watakila Morinho ya jagoranci Liverppol a gasar Premier

Watakila Jose Mourinho ya jagoranci Chelsea a karawar da za ta yi da Liverpool a gasar Premier a ranar Asabar, duk da tuhumarsa da FA take yi kan rashin da'a.

Kocin yana fustantar hukunci daga hukumar kwallon kafar Ingila, saboda korarsa da aka yi daga bencin a karawar da West Ham ta samu nasara da ci 2-1.

An kori Mourinho da mataimakinsa Silvino Louro da kuma dan wasansa Nemanja Matic daga cikin wasan a karawar.

Mourinho mai shekaru 52, ya shigar da korafi ga hukumar FA kan tuhumarsa da take yi.

Hukumar ta FA ta kuma tuhumi Chelsea da West Ham kan yadda kungiyoyin biyu suka kasa tsawatar wa 'yan wasansu, kuma ta ba su zuwa ranar Alahamis domin su kare kansu.