Paul Scholes ya soki salon koci Van Gaal

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Paul Scholes shi ne tsohon dan kwallon Manchester United

Tsohon dan kwallon Manchester United, Paul Scholes, ya ce ba zai ji dadin murza leda a karkashin koci Loius van Gaal ba.

United ta fice daga gasar Capital One Cup bayan da Middlesbrough ta doke a bugun fenariti a karawar da suka yi a ranar Laraba a Old Trafford.

Sai dai kuma Scholes ya yaba da yadda masu tsaron bayan United suka taka leda, inda ya ce an ba su horo na gari, amma ya soki salon taka leda da kungiyar ke yi.

Scholes wanda ya buga wa United wasanni 718 ya ce United ba ta murza leda kamar yadda ya dace, sannan ba ta samun damarmakin zura kwallaye a raga.

Manchester United za ta ziyarci Crystal Palace a gasar Premier wasan mako na 11 da za su buga a ranar Asabar.