Oliseh ya gayyaci 'yan wasa 23 Super Eagles

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kociyan Super Eagles Sunday Oliseh

Kociyan tawagar kwallon kafar Nigeria ta Super Eagles, Sunday Oliseh ya gayyaci 'yan wasa 23, domin fafatawa da Swaziland a wasan neman gurbin a Gasar cin Kofin Duniya ta 2018.

A cikin 'yan wasan da aka gayyata har da Obafemi Martins, wanda rabon da ya buga wa Super Eagles tamaula shekaru biyu da suka wuce kenan.

Akwai kuma 'yan wasa shida da suke murza leda a gida da kuma suka samo wa Nigeria tikitin shiga Gasar cin Kofin Nahiyar Afirka da za a yi a Rwanda a shekara mai zuwa.

Karawar da Super Eagles za ta yi gida da waje, za ta fara da ziyartar Lobamba a ranar 13 ga watan Nuwamba, sannan ta karbi bakuncin wasa na biyu a ranar 17 ga watan Nuwamba a Fatakwal.

Oliseh ya umarci dukkan 'yan wasa da ya bai wa goron gayyata da su isa otal din Bolton White Apartment da ke Abuja, Nigeria, a ranar 8 ga watan Nuwamba domin fara yin atisaye.

Ga jerin 'yan wasan da Oliseh ya gayyata Super Eagles:

Masu tsaron raga: Carl Ikeme (Wolverhampton Wanderers, Ingila); Ikechukwu Ezenwa (Sunshine Stars); Dele Alampasu (Club de Sportivo Feirense, Portugal)

Masu tsaron baya: Abdullahi Shehu (Uniao da Madeira, Portugal); Kalu Orji (Enugu Rangers); Elderson Echiejile (AS Monaco); Chima Akas (Sharks); Leon Balogun (FSV Mainz, Jamus); Godfrey Oboabona (Caykur Rizespor, Turkiya); Efe Ambrose (Celtic, Scotland); Austin Oboroakpo (Abia Warriors)

Masu wasan tsakiya: Ogenyi Onazi (SS Lazio, Italy); Paul Onobi (Sunshine Stars); John Mikel Obi (Chelsea, Ingila); Rabiu Ibrahim (AS Trencin, Slovakia); Wilfred Ndidi (KRC Genk, Belgium); Sylvester Igbonu (UFA, Rasha)

Masu zura kwallo a raga: Ahmed Musa (CSKA Moscow, Rasha); Moses Simon (KAA Gent, Belgium); Odion Ighalo (Watford, England); Ezekiel Bassey (Enyimba); Alex Iwobi (Arsenal, England); Obafemi Martins (Seattle Sounders, Amurka)