'Chamberlain da Walcott za su yi jinya'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Arsene Wenger

Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya ce Theo Walcott da Alex Oxlade-Chamberlain ba za su buga wasanni uku ba saboda raunukan da suka samu.

A ranar talata aka fitar da 'yan wasan daga fili, a yayin da suke buga wasa da Sheffield inda aka ci su uku ba ko nema a wasan.

Kenan, 'yan wasan ba za su buga wasa da Swansea da Tottenham da kuma Bayern Munich ba a wasan Champion League da kuma wasan sada zumunta tsakanin Ingila da Spaniya da kuma Faransa.

Wenger ya ce "Yanzu sun fita daga wasannin sai bayan sun huta."

Oxlade-Chamberlain mai shekaru 22, ya samu ya samu rauni a kafa yayin da shi ma Walcott ya samu rauni a kafar sa.

A ranar 13 ga watan Nuwamba, Ingila za ta buga wasan sada zamunta a Spain, yayin da za ta yi wani wasan kuma a gida tare da Faransa.