Klopp ya ce Mourinho mutumin 'kirki ne'

Image caption Kocin Kulob din Liverpool Jurgen Klopp

Kocin Liverpool, Jurgen Klopp ya ce Jose Mourinho zai iya zama mutumin kirki, tunda shi ba alkalin wasa ko dan jarida ba ne.

Kungiyoyi biyu za su hadu a ranar Asabar, a yayin da Klopp ya ke neman samun nasara a gasar Premier.

An tuhumi Kocin Chelsea, Mourinho har sau biyu a kakar gasar bana saboda kalubalantar alkalan wasa da kuma nuna rashin da a, sai dai kuma Klopp ya ce a zahiri ba halayyar Mourinho ba ne rashin da'a.

"Ina girmama ayyukan sa. Ina ga idan kai ba dan jarida ko alkalin wasa bane, Mourinho mutumin kirki ne," in ji Klopp.

Ya kara da cewa "Ni ba daya daga cikin wadanda na lissafa ba ne, saboda haka mun tattauna da shi sosai shi ya sa na gano haka".