Arsenal ta doke Swansea 3-0 a Liberty

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsenal za ta kara da Bayern Munich a gasar cin kofin zakarun Turai

Arsenal ta ci Swansea 3-0 a gasar Premier wasan mako na 11 da suka fafata a ranar Asabar a filin wasa na Liberty.

Olivier Giroud ne ya fara ci wa Arsenal kwallon farko, sannan Laurent Koscielny ya ci ta biyu.

Joe Campbell wanda ya fara buga wa Arsenal wasan Premier na farko tun lokacin da ta sayo shi a shekarar 2011 ne ya kara ta uku a raga.

Nasarar da Arsenal ta samu ya sa tana da maki iri daya dana Manchester City, amma tana mataki na biyu da tazarar kwallaye.

Arsenal din za ta karbi bakuncin Tottenham a wasan mako na 12 da za su kara a Emirates.

Ga sakamakon wasannin da aka buga:

  • Chelsea 1 - 3 Liverpool
  • Crystal Palace 0 - 0 Man Utd
  • Man City 2 - 1 Norwich
  • Newcastle 0 - 0 Stoke
  • Watford 2 - 0 West Ham
  • West Brom 2 - 3 Leicester