Zan cigaba da horas da Chelsea - Mourinho

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea tana mataki na 15 a kan teburin Premier da maki 11

Jose Mourinho ya ce zai ci gaba da jan ragamar Chelsea, zai kuma dawo da tagomashin kungiyar duk da halin da ta tsinci kanta a kakar wasannin bana.

Chelsea ta yi rashin nasara a hannun Liverpool da ci 3-1 a gasar Premier wasan mako na 11 da suka fafata a Stamford Bridge a ranar Asabar.

Doke Chelsea da aka yi ya sa tana mataki na 15 a kan teburin Premier da maki 11, kuma tuni aka fitar da ita daga gasar League Cup a ranar Talata.

Mourinho bai taba yin rashin nasara a wasanni shida a kakar wasa ba, tun lokacin da ya fara horas da Chelsea.

Kociyan ya ce idan har ya ci gaba da aiki a Stamford Bridge, zai cigaba da jajircewa domin ya dawo da martabar Chelsea a fagen tamaula.

Chelsea za ta karbi bakuncin Dynamo Kiev a wasan gasar cin kofin zakarun Turai, sannan ta ziyarci Stoke City wacce ta fitar da ita daga gasar League Cup domin buga wasan Premier mako na 12.