Na damu da rashin cin kwallaye - Van Gaal

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption United tana mataki na hudu a kan teburin Premier da maki 21

Kociyan Manchester United, Louis van Gaal ya ce ya damu da rashin cin kwallaye da kungiyar ke fuskanta a wasannin da take yi.

Kocin ya fadi hakan ne bayan da suka tashi wasa canjaras da Crystal Palace a Selhust Park a ranar Asabar a gasar Premier wasan mako na 11 da suka yi.

A wasan mako na 10 United ta buga canjaras da Manchester City a Old Trafford, haka ma ta tashi wasa babu ci da Middlesbrough wacce ta fitar da ita daga Capital One Cup a ranar Laraba.

Van Gaal ya ce "Ina cikin damuwa da rashin cin kwallaye da United ke yi, kuma tun bayan karawar mu da Middlesbrough na fadi hakan".

United tana mataki na hudu a kan teburin Premier da maki 21, za kuma ta karbi bakuncin CSKA Moscow a wasan gasar cin kofin zakarun Turai.