Caf Championleagu: TP Mazembe ta ci USM Alger

Hakkin mallakar hoto farouk batichen getty
Image caption A ranar Lahadi za a buga wasan karshe na biyu a gasar cin kofin zakarun Afirka

TP Mazembe ta samu nasara a kan USM Alger da ci 2-1 a gasar cin kofin zakarun Afirka wasa na farko da suka buga a ranar Lahadi a Algeria.

Dan kasar Zambiya Rainford Kalaba da na Tanzaniya Mbwana Samata ne suka ci wa Mazembe kwallayen, yayin da Mohamed Seguer ya farke wa USM kwallo guda.

A karawar an bai wa dan kwallon Mazembe, Kalaba da kuma dan wasan USM, Hocine El Orfi jan kati a fafatawar.

A ranar Lahadi ce TP Mazembe za ta karbi bakuncin USM Alger a wasa na biyu a Janmhuriyar Congo, kuma Mazembe ta lashe kofin sau hudu jumulla.

Duk wacce ta samu nasarar lashe kofin zakarun nahiyar Afirka za ta karbi ladan kudi dala miliyan daya da rabi, sannan ta wakilci Afirka a gasar cin kofin zakarun nahiyoyin duniya ta bana da za a yi a Japan.