Sakamakon wasannin damben gargajiya na Lahadi

Image caption Garkuwan Mai Caji ne ya kashe Shagon Na Manu a turmi na biyu

Wasanni goma aka dambata a safiyar ranar Lahadi a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Abuja, Nigeria.

Karawar da aka yi kisa ita ce wacce Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa da ya kashe Shagon Shagon Kato Mai Karfi daga Kudu a turmin farko.

Sai kuma Bahagon Soja daga Arewa da ya kashe Dogon Kato Mai Karfi daga Kudu shima a turmin farko, da kuma wasan da Garkuwan Mai Caji daga Kudu da ya buge Shagon Na Manu daga Arewa a turmi na biyu.

Dambatawa tsakanin Dogo Mai takwasara daga Arewa da Shagon Dan Digiri daga Kudu ta zo da takaddama, domin a turmin farko Shagon Dan Digiri ya dafa kasa a dukan da ya ji, amma aka ce a sake karawa domin ba za a zagaya ga 'yan kallo ba.

Dogo Mai Takwasara ya amince su sake dambatawar, amma daga baya masu marawa Kudawa baya suka ce sun amince da an kashe Shagon Dan Digiri a wasan.

Shima Fijot daga Arewa ya kashe Shagon Shagon Mada daga Kudu a turmi na biyu.

Ga jerin wasannin da ba a yi kisa ba:

  1. Shagon Dan Jimama daga Kudu da Shagon Garba Dan Malumfashi daga Arewa
  2. Shagon Buzu daga Arewa da Shagon Bahagon Babangida daga Kudu.
  3. Autan Faya daga Kudu da Shagon Bahagon Musa Arewa
  4. Habu na Shagon Dutsen Mari da Sama'ila Shagon Alabo daga Kudu
  5. Sanin Kwarkwada daga Kudu da Shagon Shagon Alhazai daga Arewa.