Rafinha na daf da tsawaita zamansa a Barcelona

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rafinha ya fara buga wa babbar kungiyar Barcelona wasa a 2011 ya kuma buga mata sau 27 ya ci kwallo 1

Rafinha zai sake rattaba hannu kan yarje-jeniyar da zai cigaba da taka wa Barcelona leda zuwa 30 ga watan Yunin 2020.

Haka kuma Barcelona za ta sabunta yarje-jeniyar kudi £53.5m ga duk kungiyar da take son daukar dan wasan idan har kwantiraginsa da Barcelona bai kare ba.

Rafinha dan kasar Brazil mai shekara 22, ya fara wasa da karamar kungiyar Barcelona a inda ta bayad da shi aro ga Celta Vigo.

Dan wasan ya fara yi wa tawagar kwallon kafar Brazil wasa a watan Satumbar 2015, yanzu kuma yana yin jinyar raunin da ya ji a karawa da suka yi da Roma a watan na Satumbar.

Dan uwan Rafinha wanda ke buga wa Spaniya tamaula Thiago Alcantara yana murza leda a kungiyar Bayern Munich ta Jamus.