Arsenal za ta kara da Munich a kofin zakarun Turai

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsenal tana mataki na biyu a kan teburin Premier

Arsenal za ta ziyarci Bayern Munich a wasa na biyu na gasar cin kofin zakarun Turai da za su fafata a ranar Laraba.

A karawar farko da suka yi gumurzu a Emirates a rukuni na shiga na gasar kofin zakarun Turan, Arsenal ce ta doke Munich da ci 2-0 a ranar Talata 20 ga watan Oktoba.

Bayan da kungiyoyin suka buga wasanni uku kowannensu, Munich ce ke mataki na daya da maki 6, ita ma Olympiacos tana da maki 6 a matsayi na biyu, yayin da Arsenal da NK Dinamo Zagreb suke da maki uku-uku kowannensu.

Chelsea wacce ta tashi canjaras da Dynamo Kyiv a Ukraine, za ta karbi bakuncin wasa na biyu a Stamford Bridge.

Bayer Leverkusen wacce ta tashi 4-4 da Roma za ta ziyarci Italiya a karawa ta biyu, sai Barcelona da ta doke FC Bate 2-0 za ta karbi bakunci wasa na biyu a Camp Nou.

Ga wasannin da za a buga:

Chelsea FC - England vs FC Dynamo Kyiv - Ukraine AS Roma - Italy vs Bayer Leverkusen - Germany FC Barcelona - Spain vs FC Bate Borisov - Belarus Bayern Munich - Germany vs Arsenal FC - England Olympique Lyonnais - France vs Zenit St. Petersburg - Russia Olympiacos CFP - Greece vs NK Dinamo Zagreb - Croatia Maccabi Tel Aviv FC - Israel vs FC Porto - Portugal KAA Gent - Belgium vs Valencia C.F - Spain