Ba zan yi wa Mourinho tawaye ba — Fabregas

Hakkin mallakar hoto
Image caption Dan wasan tsakiya na kulob din Chelsea Cesc Fabregas

Dan wasan tsakiya na kulob din Chelsea Cesc Fabregas ya musanta zargin da kafafen yada labarai ke yi cewa ya shirya yiwa Kocin Kulob din Jose Mourinho tawaye.

Wani Shafin yada labarai na 'yan wasan kwallon kafa na sirri ya yi ikirarin cewa Cesc Fabregas shi ne jagoran shirya wani dan karamin tawaye da aka shira yi wa kulob din.

Cesc Fabregas ya yi bayani a shafinsa na Twitter cewa, "Ina so na yi sharhi a kan wasu rahotanni da wasu kafafen yada labarai suka wallafa, ni ina jin dadin kasancewa ta a Chelsea, sannan kuma akwai kyakkyawar dangantaka tsakanina da kocin".

Ya cigaba da cewa "akwai wasu mutane da ke kokarin kawo rudani a kungiyarmu, amma na yi amanna cewa ba zamu bari su cimma burinsu ba".

Kare kofin da Chelsea take yi na Capital one ya zo karshe a makon daya gabata, bayan da aka doke ta da ci 5-4 a bugun Fanareti.