Netherlands ba ta gayyaci Depay da Van Persie ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Netherlands ba ta samu tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da za a yi a Faransa a badi ba

Tawagar kwallon kafa ta Netherlands ba ta gayyaci Memphis Depay da kuma Robin van Persie cikin 'yan wasan da za su buga mata wasan sada zumunta da Wales ba.

Wales ce za ta karbi bakuncin Netherlands a wasan sada zumunta da za su fafata a filin wasa na Cardiff ranar 13 ga watan Nuwamba.

Depay mai taka leda a Manchester United ya ci kwallaye 19 a kungiya da kasarsa, yayin da Van Persie mai murza leda a Fenerbahce ya zura biyar a raga daga wasanni 16.

Sai dai kuma Netherlands din wacce ta kasa samun gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da za a yi a Faransa a badi, ta gayyato Arjen Robben wanda ya warke daga jinya.

Wales ta samu tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da za a yi a 2016, kuma rabon da ta halarci babbar gasar kwallon kafa tun ta kofin duniya da ta buga a 1958.

Ga jerin 'yan wasan da Netherlands ta gayyata:

Mai tsaron raga: Jasper Cillessen (Ajax), Maarten Stekelenburg (Southampton), Kenneth Vermeer (Feyenoord), Jeroen Zoet (PSV).

Masu tsaron baya: Jeffrey Bruma (PSV), Virgil van Dijk (Southampton), Daryl Janmaat (Newcastle United), Terence Kongolo (Feyenoord), Karim Rekik (Marseille), Jairo Riedewald (Ajax), Kenny Tete (Ajax), Joel Veltman (ajax).

Masu buga tsakiya: Daley Blind (Manchester United), Vurnon Anita (Newcastle United), Jordy Clasie (Southampton), Davy Klaassen (Ajax), Wesley Sneijder (Galatasaray), Marko Vejinovic (Feyenoord), Georginio Wijnaldum (Newcastle United).

Masu cin kwallaye: Bas Dost (Wolfsburg), Eljero Elia (Feyenoord), Anwar El Ghazi (Ajax), Luuk de Jong (PSV), Quincy Promes (Spartak Moscow), Arjen Robben (Bayern Munich).