Magoya bayan Al Ain sun yi wa Emenike ihu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Emenike ya yi ritaya daga buga wa Super Eagles tamaula

Kociyan Al Ain, Zlatko Dalic ya bukaci magoya bayan kungiyar da su marawa Emmanuel Emenike baya, bayan da suka yi masa ihu a gasar wasan da suka yi ranar Asabar.

Emenike wanda ya koma Al Ain da taka leda aro daga Fenerbahce ya ci kwallaye hudu a wasanni bakwai da ya buga gasar cin kofin kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.

Sai dai kuma magoya bayan kungiyar sun yi wa Emenike ihu a lokacin da aka sauya shi daga wasa a minti na 86 a karawar da suka yi da Al Jazira.

Koci Dalic ya ce ba zai ji dadin halayyar wasu magoya bayan kungiyar ba, duk da cewa sun lashe wasa sun kuma taka leda mai kayatarwa, amma aka yi wa Emenike ihu.

Emenike ya koma Al Ain a cikin watan Yuli a inda ya maye gurbin Asamoah Gyan, wanda ya ci wa kungiyar kwallaye 128.

Haka kuma Gyan din ya lashe kofin gasar kasar sau uku, bayan da ya zama dan wasan da ya fi yawan cin kwallaye a gasar a shekara uku daga cikin hudun da ya yi.

Dalic ya ja kunnen magoya bayan kungiyar da cewar kar su taba zaton Emenike zai iya samun nasarorin da Gyan ya yi a kungiyar.

Emenike ya yi ritaya daga buga wa tawagar kwallon kafa ta Nigeria, wato Super tamaula.