Munich ta casa Arsenal 5-1 a gasar kofin Turai

Image caption Arsenal za ta karbi bakuncin Dinamo Zagrev a ranar 24 ga watan Nuwamba

Bayern Munich ta lallasa Arsenal da ci 5-1 a gasar cin kofin zakarun Turai da suka kara a ranar Laraba a Jamus.

Munich din ta fara cin kwallo ta hannun Lewandowski a minti na 10 da fara tamaula, Muller ne ya kara ta biyu a minti na 29 kuma ya ci ta biyar, sai Alaba da ya kara ta uku daf da za a je hutun rabin lokaci.

Bayan da aka dawo ne daga hutu Roben ya ci ta hudu, sai kuma Arsenal ta zare kwallo daya ta hannun Giroud a minti na 24 da dawo wa daga hutun.

Da wannan sakamakon Bayern Munich tana mataki na daya a kan teburi a rukuni na shida da maki tara, sai Olympiacos da ita ma ke da maki tara, Arsenal da Dinamo Zagreb kowannensu na da maki uku-uku.

Ga sakamakon wasannin da aka buga:

  • Barcelona 3 - 0 BATE Bor
  • Chelsea 2 - 1 Dynamo Kiev
  • Roma 3 - 2 Bayer Levkn
  • Olympiakos 2 - 1 Dinamo Zagreb
  • M'bi Tel-Aviv 1 - 3 FC Porto
  • KAA Gent 1 - 0 Valencia
  • Lyon 0 - 2 Zenit St P