QPR ya kori kociyansa Chris Ramsey

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kungiyar QPR ta sallami kociyanta Chris Ramsey.

Kolob din Queens Park Rangers ya kori kociyansa Chris Ramsey daga kociyan kungiyar .

Kociyan, mai shekaru 53, wanda ya sanya hannu a kan kwantiragin shekara uku a watan Mayu bayan da ya yi shugabancin rikon kwarya, an sallame shi ne kwana daya bayan kungiyar Derby ta ci su daya mai ban haushi wanda hakan ya jawo kungiyar ta zama ta 13 a teburin gasar Zakarun Turai.

Daraktan kungiyar ta QPR Les Ferdinand, ya ce an dauki wannan matakin ne domin ciyar da kungiyar gaba.

An bai wa Neil Warnock, wani tsohon kociyan rikon kungiyar na wucin gadi.

A wata sanarwar da kungiyar ta fitar a shafin intanet dinta, ta ce kwana-kwanan nan za ta fitar da gurbin neman aikin wanda zai maye gurbin Mista Ramsey.