Ba zan daukaka kara ba - Mourinho

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mourinho ya ce ba zai daukaka kara kan dakatarwar da aka masa ba.

Kocin Chelsea, Jose Mourinho ya ce ba zai daukaka kara ba a kan dakatarwar da aka yi masa a wasansu da Stoke ranar Asabar.

Hukumar kwallon Ingila, FA ta zartar da hukuncin ne ga Mourinho mai shekaru 52, saboda a ladabtar da shi ga tsaurin ido da ya nuna wa alkalan wasa lokacin da Chelsea ta sha kashi da ci biyu da daya a hannun West Ham.

Mourinho ba shi da damar shiga filin wasan Britannia Stadium, amma zai taho da tawagar 'yan wasan sa, kuma yana da damar sauye- sauye lokacin wasan.

"Na hakura," In ji Mourinho. "Ba amfanin kalubalantar su domin ba za a yi nasara ba".

Daga bisani an tambaye shi ko yaya ya ji bayan an dakatar da shi ? Sai ya ce "Ai ka san abu ne mai wuya, saboda haka ka san ban ji dadi ba."