Netherlands ba ta gayyaci Memphis da Van Persie ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Netherlands ba ta gayyaci van Persie da Memphis ba.

Netherlands ba ta gayyaci Memphis Depay da Robin van Persie a cikin tawagarta domin buga wasan sada zumunci tsakaninsu da Wales a filin wasan Cardiff City, a ranar 13 ga watan Nuwamba.

A kakar wasannin bana, Depay, dan shekaru 21, mai wasa a kulob din Manchester United, ya zura kwallaye 4 a wasanni 19, yayin da van Persie wanda ke murza leda a Fenerbahce ya sha biyar cikin wasanni 16.

Kocin Netherlands, Danny Blind, ya yi tsokaci kan Depay, inda ya ce,"Dole ka zama mai kuzari a kwallo, kuma shi ba haka ya ke ba, dole ya dauki darasi ka hakan".

Netherlands ta dawo da kyaftin din ta Arjen Robben, wanda ya ke hutun rauni da ya samu, bayan rashin yin fice da ta yi a gasar Euro da za a buga a shekarar 2016 ba, inda ta kare na hudu a gasar.