U 17: Nigeria ta lallasa Mexico

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Nigeria ta lallasa Mexico da ci 4-2, yayin da da Mali ta ci Belgium da ci 3-1.

Najeriya za ta kara da Mali ranar Lahadi a wasan karshe na gasar cin kofin kwallon kafar Afirka na 'yan kasa da shekaru 17.

Za a yi wasan ne a kasar Chile.

Hakan na zuwa ne bayan Nigeria ta lallasa Mexico da ci 4-2, yayin da Mali ta ci Belgium da ci 3-1 a wasan kusa da na karshe.

Dan kwallon Najeriya Orji Okwonkwo na cikin fitattun masu zura kwallo a raga, tare da Osinachi Ebere wanda shi ma ya yi fice a gasar kwallon kafa ta duniya.

Boubacar Troare da Sekou Koita na Mali za su buga wasan.