Saliyo za ta iya karbar wasannin kwallon kafa

Hakkin mallakar hoto Sta Kambou Getty
Image caption Sama da mutane 8,704 ne suka kamu da cutar Ebola a Saliyo kuma 3,589 suka rasa rayukansu

A ranar Asabar ce hukumar lafiya ta duniya ta wanke Saliyo daga cikin kasashen da ke da cutar Ebola.

Hakan kuma na nufin kasar za ta iya karbar bakuncin kasashe a wasannin kwallon kafa.

Rabon da Saliyo ta buga babban wasa a kasarta tun ranar 19 ga watan Yulin 2014, lokacin da ta ci Seychelles a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da aka yi a shekarar 2015.

Hukumar kwallon kafa ta Afirka ce CAF ta saka takunkumin buga wasa a Saliyo watanni 15 da suka wuce domin kaucewa yaduwar cutar Ebola.

Haka kuma hukumar ta CAF ta kara saka wasu takunkumin karabar bakuncin wasannin kwallon kafa ga Guinea da Liberia.

An amincewa kasar Liberia da ta karbi bakunci wasanni da za ta yi a gaba, saboda wanke ta da aka yi daga cutar Ebola watanni shida da suka wuce.