Horo ya fafata da Nakande a damben gargajiya

Image caption Dambatawar da suka yi babu kisa a turmi biyu da suka yi

Sarkin Dambe Ashiru Horo ya kara da Nakande a wasan damben gargajiya da suka fafata a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Abuja Nigeria.

Dambatawar ba ta kayatar ba ganin yadda Horo dan damben Arewa ya ki sakar jikinsa a wasan da suka yi turmi biyu da Nakande dan wasan Kudu.

Sauran wasannin da aka yi a ranar Lahadi da safen sun hada da karawar da Dogo Dan Shahada ya kashe Shagon Bahagon Musa daga Arewa.

Ga wasannin da aka tashi babu kisa:

  1. Audu Na Maikashi daga Kudu da Bahagon Musan Kaduna daga Arewa
  2. Garkuwan Shagon Mada daga Kudu da Na Doron Baga daga Arewa
  3. Garkuwan Shamsu daga Arewa da Garkuwan Shagon Alabo daga Kudu
  4. Nura Dan Karami daga Arewa da Garkuwan Mai Caji daga Kudu
  5. Fijo daga Arewa da Bahagon Dakakin Dakaka daga Kudu
  6. Garkuwan Shagon Alabo daga Kudu da Basiru Shagon Batau daga Arewa
  7. Autan Faya daga Kudu da Shagon Musan Kaduna daga Arewa