Falconets ta samu gurbin buga gasar kofin duniya

Tawagar kwallon kafa ta mata ta Nigeria 'yan kasa da shekara 20, Falconets ta samu tikitin shiga gasar kofin duniya ta mata, bayan da ta ci Afirka ta Kudu daya mai ban haushi har gida.

Falconets din ta ci Afirka ta Kudu ne a minti na 16 da fara tamaula ta hannun Chinwendu Ihezuo, kuma a wasan farko da suka yi a Nigeria, Falconets ce ta ci 2-1.

Kasar Ghana ce ta samu daya tikin, bayan da ta ci Habasha 4-0 a filin wasa na Baba Yara da ke Ghana, a wasan farko a Habasha 2-2 suka buga.

Za a buga gasar cin kofin duniya ta mata 'yan kasa da shekara 20 a Papua New Guinea a shekara mai zuwa.