Nigeria ta lashe gasar FIFA ta U-17

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan wasan kungiyar Golden Eaglets ta Najeriya

'Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Golden Eaglets na Najeriya sun sake daukar kofi a gasar FIFA ta 'yan kasa da shekaru 17, bayan da suka lallasa kasar Mali da ci 2- 0, a birnin Vina Del Mar na kasar Chile .

Dan wasan kwallon kafa na Najeriya, Victor Osimhen ne ya soma zira kwallo a cikin raga, yayin da Funsho Banboye ya saka kwallo ta biyu bayan wasu yan dakikoki.

Haka kuma Samuel Diarra ya kare gidansa lokacin da alkalin wasa ya ba Najeriya bugun daga- kai-sai mai-tsaron gida.

Wannan dai shi ne karo na biyar da Najeriyar take daukar wannan kofin.