New York City ta nada Patrick Vieira kociyanta

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Viera ya taka leda a Arsenal sannan ya koma Manchester City

New York City ta Amurka ta nada tsohon dan wasan Arsenal da Manchester City, Patrick Vieira, a matasyin sabon kociyan kungiyar.

Vieira mai shekaru 39 ya bar aikin horar da karamin kulob din Manchester City, a inda ya saka hannu kan yarjejeniyar shekaru uku da New York.

Kungiyar New York City tana cikin rukunan kungiyoyin kwallon kafa mallakin Sheik Mansour mai kulob din Manchester City.

Vieira zai fara aikin horas da New York City mai buga gasar Amurka a ranar daya ga watan Janairun 2016.

New York City tana da fitattun 'yan wasa da suka taka mata leda da suka hada da tsohon dan kwallon Chelsea Frank Lampard da na Juventus Andrea Pirlo.