Real Sociedad ta kori Moyes daga aiki

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Saura kwana daya ya rage wa Moyes ya cika shekara daya a Real Sociedad

Real Sociedad ta sallami David Moyes daga aikin horar da ita kwana daya da ya rage ya cika shekara daya tare da kungiyar dake Spaniya.

Moyes mai shekaru 52, ya jagoranci Real Sociedad kai ta mataki na 12 a kan teburin Spaniyar bara tun sanda ya koma can da aiki a ranar 10 ga watan Nunambar 2014.

A kakar bana kuma Real Sociedad tana mataki na 16 a kan teburi, kuma a ranar Juma'a Las Palmas ta ci ta 2-0.

Kungiyar ta nada mataimakin Moyes, Billy McKinlay, a matsayin kociyan rikon kwarya.

Kungiyar za ta buga wasannin La Liga biyu nan gaba da Sevilla da kuma Barcelona.