Vardy ya samu kyautar gwarzon watan Oktoba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Vardy na haskaka a gasar Premier ta bana

An bayyana dan kwallon Leicester City, Jamie Vardy a matsayin gwarzon dan kwallon gasar Premier na watan Oktoba.

Dan wasan Ingila mai shekaru 28, ya zura kwallaye 12 a wasanni 12 inda ya taimaka wa Leicester ta kasance ta uku a kan jadawalin gasar Premier.

Vardy na daga cikin 'yan wasan da kocin Ingila, Roy Hodgson ya gayyata domin buga wasannin sada zumunci da Spain da kuma Faransa.

Shi kuma kocin Arsenal, Arsene Wenger ya samu kyautar a bangaren masu horas da 'yan kwallo bayan da ya lashe wasanni hudu a cikin karawa hudu.

Wannan ne karo na 15 da Wenger ya samu wannan kyautar.