Payet zai yi jinyar watanni uku

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jinyar Payet, cikas ne ga West Ham

Dan kwallon West Ham, Dimitri Payet zai yi jinyar watanni uku saboda rauni a idon sawunsa.

Dan wasan na Faransa, ya ji rauni a kafarsa ta hagu bayan da, ya yi karo da dan kwallon Everton, James McCarthy a wasan da suka tashi kunen doki a filin Upton Park.

Payet mai shekaru 28, ya zura kwallaye 5 a wasanni 14 da ya buga wa West Ham tun bayan da ta siyo shi daga Marseille a kan fan miliyan 10.7.

A yanzu dai West Ham ce ta shida a kan jadawalin gasar Premier.

Shi ma dan kasar Ecuador, Enner Valencia zai yi doguwar jinya bayan da ya ji rauni.