Ibrahimovic ya sake lashe kyauta a Sweden

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ibrahimovic ya kafa bajinta a Sweden

Dan kwallon Sweden, Zlatan Ibrahimovic ya sake lashe kyautar gwarzon dan wasan kasarsa a karo na goma.

Dan wasan wanda ke taka leda a Paris St-Germain, ya lashe kyautar sau tara kenan a jere.

Babu dan wasan da ya taba lashe gasar sau biyu a tarihi ban da Ibrahimovic.

A bana, Ibrahimovic ya lashe kofuna uku a gasar Faransa kuma a tarihi shi ne ya fi kowanne zura kwallaye a kungiyar PSG.

Ibrahimovic ya murza leda a Juventus da Inter Milan da Barcelona da AC Milan da kuma PSG.