An garzaya da Sepp Blatter Asibiti

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A cikin watan Fabrairu ne za ayi zaben sabon shugaban da zai jagoranci Fifa

An kai Sepp Blatter shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa wanda aka dakatar asibiti, sakamakon rashin lafiya mai tsanani.

An dakatar da Blatter mai shekaru 79, wanda ya ja ragamar hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa shekara 18 daga shiga harkokin hukumar zuwa kwanaki 90.

BBC ta gano cewa Mr Blatter ya na fama da abin da aka kwatanta a matsayin wata 'yar sarewa kuma jikinsa na bari.

Mahukuntan Switzerland na gudanar da bincike a kan Mr Blatter, kan zarge zargen cin hanci, abin da ya musanta.

Kwamitin ladabtarwa ne na hukumar Fifa ya dakatar da Blatter da kuma shugaban hukumar kwallon kafar Turai Michel Platini a farkon watan Oktoba.