Fifa ta hana Musa Bility yin takara

Image caption Musa Bility

Fifa ta yi watsi da bukatar Musa Bility dan kasar Liberia ta yin takarar shugabancin hukumar sakamakon kasa cika wasu ka'idoji na hukumar.

Hukumar gudanarwar Fifa ta amince da 'yan takarar shugabancin hukumar biyar, kuma babu shugaban hukumar kwallon kafa ta Turai, Uefa, Michel Platini wanda aka dakatar daga aiki.

Amma za a iya sanya Platini a cikin 'yan takarar shugabancin hukumar idan wa'adin dakatarwar da aka yi masa ya kare kafin zaben da za a yi a karshen watan Fabrairun badi.

Daga cikin mutane biyar din da aka amince da dakatar ta su sun hada da Yarima Ali bin al-Hussein, Jerome Champagne, Gianni Infantino, Sheikh Salman bin Ebrahim al-Khalifa da kuma Tokyo Sexwale.

Fifa ta ce ba za ta iya cewa komai ba game da cire Bility daga cikin 'yan takarar, matakin da shugaban hukumar kwallon kafa ta Liberia zai iya kalubalanta a kotun harkokin wasanni.