Ruwan sama ya hana wasan Argentina da Brazil

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu kallo sun makale a hanyar su ta zuwa filin wasan tsakanin Argentina da Brazil da aka dakatar.

An dakatar da wasan Argentina da Brazil na neman cancantar bugar gasar kwallon kafa ta duniya, kasa da sa'a daya da fara wasan, saboda ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Jami'ai a kasar Brazil sun ce filin wasan na Monumental ya cika da ambaliyar ruwa, inda masu kallo suka makale a hanyar su ta zuwa filin.

Mataimakin shugaban hukumar kwallon Brazil, Gilmar Rinaldi ya ce, "Mun tattauna da jami'an kwallon kafar da wakilan Argentina, kuma babu yadda za ayi mu ci gaba da wasan cikin wannan hali."

An saka ranar Jumma'a da misalin karfe tara, lokacin da za a sake kararwar.