FIFA ta dakatar da Mayolas da Wantete

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hukumar ta FIFA ta haramtawa Mayolas da Wantete shiga harkokinta, har tsawon watanni shida.

Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, ta haramta wa mataimakin shugaban Hukumar Kwallon Kafar kasar Congo, Jean Guy Blaise Mayolas, da sakatare janar na Hukumar, Badji Mombo Wantete, shiga harkokinta har tsawon watanni shida.

Da ma can suna fuskantar dakatarwa ta wucin-gadi sakamakon laifin da suka aikata, saboda haka haramcin na kwanaki 45 ne kawai, idan aka debe kwanakin da suka yi na dakatarwar ta wucin-gadi.

An samu Mayolas da Wantete da laifin saba ka'idar Hukumar FIFA wadda ta danganci bayarwa da kuma karbar kyaututtuka.

A kwanaki baya ne hukumar ta FIFA ta dakatar da shugaban nata Sepp Blatter, da wasu shugabannin hukumar, bisa zargin karbar hanci.