Bayanai kan Yacine Brahimi

Hakkin mallakar hoto getty
Image caption Brahimi zai iya lashe kyautar sau biyu ?

Mai rike da kyautar gwarzon dan kwallon BBC ta ba dan kasar Algeria, Yacine Brahimi na fatan lashe kyautar karo na biyu - tarihin da dan kwallon Nigeria Jay-Jay Okocha ya yi a shekarar 2003 da kuma 2004.

Hakan kuma zai fayyace cigaban da dan kwallon ke yi tun komawarsa FC Porto daga Granada ta Spaniya a watan Yunin 2014.

Dan kwallon ya shaidawa BBC cewar "Ina samun kwarewa ta yadda nake buga tamaula da manyan kungiyoyi, hakan ya sa nake koyan wasan kuma nake tashi tsaye tukuru a kowanne wasa nake yi."

Lallai kuwa hakika ya dauki awanni da dama yana saka kaimi kuwa.

Wani gagarumin cigaban da Brahimi y samu a shekarar 2014/15 shi ne buga gasar cin kofin zakarun Turai, a inda ya yi sau 42, in banda Eden Hazard na Chelsea da ya yi 51 da kuma Lionel Messi na Barcelona da suka shiga gabansa.

Kwallaye biyar da ya ci sun taimakawa Porto kai wa wasan daf da na kusa da karshe a karon farko, wanda rabaon da ta yi hakan shekaru shida da suka wuce.

Idan aka tuna gasar cin kofin zakarun Turai ta European Cup wasan karshe a shekarar 1987 Porto ce ta doge Munich da ci 3-1 a karawar farko, kafin a doke ta 6-1 a wasa na biyu.

Shi ne haskakawar da Porto ta yi a shekarar da ta kammala a mataki na biyu a gasar a inda Brahimi ya ci kwallaye bakwai a gasar ta Portugal kuma kwallaye 13 ya ci jumulla a shekarar.

Bayan da aka kammala kakar wasanni ne, Porto ta kara kudin yarjejeniya idan wata kungiyar na son daukar Brahimi idan kwantiraginsa ba ta kare ba daga Yuro miliyan 50 zuwa Yuro miliyan 60.

Koda yake har yanzu dan wasan bai ci kwallaye da dama kamar yadda yake ci a baya ba, amma ya kara samun kwarewa a kakar 2015-16 a inda ya dinga lashe dan kwallon da ya fi haskakawa a wasannin da suke yi sau da dama.

Daya daga haskakawar ita ce a watan Satumba a gasar cin kofin zakarun Turai a lokacin da ya taimaka a dukkan kwallayen da Porto ta ci Chelsea. (porto ta lashe wasanni 20 da ta yi gida).

Brahimi dan kwallon da aka yaye daga Clairefontaine ta Faransa ya kuma kara nuna kansa a inda ya ci kwallaye bakwai daga wasanni 14 da ya buga gasar cin kofin zakarun Turai.

Kamar yadda ake hasashe Brahimi zai zama daya daga cikin fitattun 'yan wasa da za su yi fice a fagen tamaula a duniya da zai bi sahun James Rodriguez da Hulk da kuma Falcao.

Yakan matsawa masu tsaron baya da juya tamaula a kuraren wuri da iya sarrafa ta da kuma dabaru da dama na salon murza leda.

Kocin Algeria, Christian Gourcuff, cewa ya yi "Ba su da yawa a fagen kwallon kafa kamar yadda yake sarrafa tamaula".

A gasar cin kofin nahiyar Afirka ne ya nuna yadda yake da hadari tare da tamaula a inda Algeria ta yi rashin nasara a wasan daf da na kusa da karshe a hannun Ivory Coast a watan Fabrairu, a inda 'yan wasan Ivory Coast suka dunga kai wa Brahimi hare-hare.

Sai da aka yi wa dan wasan keta sau bakwai a karawar da Ivory Coast ta ci su 3-1, kuma jumulla an yi masa keta kaso uku da digo bakwai a wasannin da ya buga a cikin rukuni bayan da aka kasa doke Algeria.

Duk da kasa lashe kofin nahiyar Afirka da Algeria ta yi, tun daga lokacin ne Brahimi ya ci gaba da haskakawa a fagen kwallon kafa.

Abin da masana ke cewa - Maher Mezahi, BBC Sport, Algeria:

Shin ko da akwai wanda ya iya yanka a Afirka kamar Yacine Brahimi? Da kyar ne. Haka kuma ya fahimci yadda magoya bayan Algeria ke son a murza musu tamaula a kasar da ta fi shewa kan bajinta fiye da zura kwallaye a raga. Dan kwallon Porto mai saka riga lamaba takwas sarki ne.

Hakan ne ya sa Brahimi ya dace ya lashe kyautar BBC ta bana kuma karo na biyu a jere saboda yana taka ledar da take bai