Bayanai kan Yaya Toure

Hakkin mallakar hoto getty
Image caption Burin Toure ya cika a shekarar 2015

Mafarkin dan kwallon tawagar Ivory Coast da Manchester City, Yaya Toure ya zamo gaskiya a shekarar 2015, a inda ya lashe kofin nahiyar Afirka, bayan buga gasar karo shida da ya yi.

Bayan da kasar ta kasa lashe kofin 2006 da kuma 2012 dukkansu a bugun fenariti, sai gashi ta dauka a 2015 a inda ta ci Ghana a bugun fenaritin kuma Yaya Toure ya ci kwallon da ya buga a raga.

Shekaru takwas baya da Ivory Coast ta dauki kofin Afirka a shekarar 1982, sai gashi Toure ya jagoranci tawagar lashe kofin karo na biyu.

Hakan kuma sakayyace ga daya daga cikin fitattun 'yan kwallon Afirka dake da inganci a karnin da da ya fi haskakawa.

"Tun daga shekarar 2006 mutane suke ta cewa tawagar Ivory Coast ce ta fi fice a fagen tamaula, amma ba mu dauki kofin ba" in ji Toure, wanda a karo na uku yake shiga cikinjerin 'yan takarar kyautar gwarzon dan kwallon Afirka da BBC ke karramawa.

"Shekara ta 2015 mai ban mamaki ce saboda mun dauki kofin tare da dan uwana Kolo wanda na jagoranci tawagar"

Kamar yadda ya saba a koda yaushe, Toure ya jagoranci kasarsa tun daga gurbin masu buga tsakiya a ci Jamhuriyar Congo da Boli a wasan da da karshe.

Bayan da Ivory Coast ta samu nasarar lashe kofin Afirka ta kuma koma Abidjan, Toure wanda ya lashe kuaytar ta BBC a shekarar 2013 ya riko kofin tun daga jirgi har cikin kasar wanda ya ja ragamar tawagar da ta yi rashin Didier Drogba wanda ya yi ritaya daga buga wa kasar tamaula a farkon watan. Za ku iya zabe a nan

Bayan da dan kwallon ya haska kan gudunmawar da ya bai wa kasarsa, haka kuma ya nuna amfaninsa a kungiyarsa.

Kafin ya je gasar kofin nahiyar Afirka, Manchester City tayi kan-kan-kan a mataki na daya a kan tebrurin Premier a inda Toure ya yi wasanni tara suka kuma lashe karawar.

Lokacin da Toure ke yi wa Ivory Coast wasanni City ta kasa lashe fafatawa biyar da ta yi, wanda hakan ya sa ta yo kasa a kan teburin Premier aka kuma fitar da ita daga gasar cin kofin Kalubale.

Haka City ta kammala gasar Premier 2014-15 ba tare da lashe lambar yabo ba, kuma duk da watanni biyu da Toure ya yi a gasar kofin Afirka yana daga cikin 'yan wasa uku da suka ci wa kungiyar kwallaye 10 ko fiye da haka da suka hada Sergio Aguero da kuma David Silva.

Dan wasan mai shekaru 32, ya fara buga kakar bana da karfin gwiwa, a inda ya jagorancin City ta fara kakar bana da kafar dama sannan ya buga mata dukkan wasannin cin kofin zakaraun Turai da ta kai wasan zagaye na biyu.

A cikin watan Oktoba Fifa ta saka sunansa a cikin 'yan kwallon da hukumar kwallon kafa ta duniya za ta zabi wanda ya fi yin fice a tamaula a duniya karo hudu a jere kuma karo uku da shi kadai ne dan wasa daga Afirka a cikin'yan takarar.

Hakan ya biyo bayan da Toure tabbas dan wasa ne da ba za a iya ajiye shi ba, a inda yake kara kwazo tun daga yarintarsa har zuwa lokacin da yake yanke abokan karawa a manyan wasannin gasar Turai.

City ba ta lashe kayutuka a shekaru hudu kafin Toure tsohon dan wasan Barcelona ya koma can da murza leda a 2010, tun daga lokacin ne suka dauki kofin Premier biyu da kofin kalubale da League Cup da kuma halartar kofin zakarun Turai a kai a kai.

Abin da masana ke cewa - Oluwashina Okeleji, BBC African Sport:

An zabo Yaya Toure a cikin 'yan takarar da BBC za ta karrama a bana kuma kyautar da ya lashe a shekarar 2013, kuma sau bakwai yana shiga cikin 'yan takara. Ana mai hangen cewa daya ne daga cikin wanda ya dara sara a karni a cikin sawun masu taka leda daga tsakiyar fili, wanda ya nuna amfaninsa a kasarsa da kuma kungiyarsa a shekarar 2015.

Dan wasan ne da tabbar da ya mamaye abokin wasa da karfi tuwo a fagen tamaula, Toure ya saba cin wasanni - a watan Fabrairu ya jagoranc Ivory Coast ta lashe kofin nahiyar Afirka.

Shi kadai ne tilo daga Afirka da yake takarar dan kwallon da Fifa za ta karrama a matsayin wanda ya fi yin fice a duniya daga cikin 'yan wasa 23 da ta fitar, kuma yake nuna cewar shi ne dan wasan Afirka da ya fi haskakawa. Dalilin da ya sa dan wasan tawagar Ivory Coast ya kamata ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na BBC a karo na biyu.