Blackburn Rovers ta nada Paul Lambert kociyanta

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A cikin watan Fabrairu Aston Villa ta sallami Lambert daga aiki

Blackburn Rovers ta nada tsohon kociyan Aston Villa, Paul Lambert a matsayin kociyanta domin ya maye gurbin Gary Bowyer wanda ta sallama daga aiki.

Lambert mai shekaru 46, shi ne mai horas da 'yan wasan tamaula na bakwai da Blackburn ta dauka a cikin shekaru bakwai.

Blackburn ta sallami Bowyer a ranar 10 ga watan Nuwamba, bayan da ya ci wasa biyu daga guda 10 da ya fafata, da hakan ya kai kungiyar mataki na 16 a kan teburin gasar Championship.

Tsohon dan wasan Rovers kuma kociyan karamar kungiyar Alan Irvine an bashi mataimakin koci, shi ma tsohon mai horar da matasan kungiyar Rob Kelly ya dawo cikin tawagar masu horar da Blackburn din.