Ina son sake horas da tamaula a Premier - Ancelotti

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Carlo Ancelotti dan kasar Italiya yana yin hutu a Vancouver a yanzu haka

Tsohon kociyan Chelsea, Carlo Ancelooti ya ce yana da sha'awar ya sake horas da kwallon kafa a Premier, amma ba a wannan kakar wasan ba.

Ancelotti mai shekaru 56, wanda ya lashe kofin Premier da FA a shekarar 2010, shi ne ake rade-radin cewar zai maye gurbin Manuel Pellegrini a Manchester City.

Sai dai kociyan ya ce ba zai dawo horas da tamaula a gasar ta bana ba, wanda hakan ya kawo karshen jita-jitar cewar daf yake da maye gurbin Jose Mourinho a Chelsea.

Tsohon kociyan Paris St-Germain da kuma Real Madrid ya kara da cewar ya ji dadin aikin da ya gudanar a kasar Faransa da kuma Spaniya.

Yanzu haka Ancelooti yana yin hutu a Vancouver tun lokacin da Real Madrid ta sallame shi daga aiki a 2015, shekara daya bayan da ya lashe kofin zakarun Turai.