Euro 2016: Ba za mu dage wasanni ba

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane 129 suka mutu, 350 suka ji raunuka a hare-haren da aka kai Faransa a ranar Juma'a

Jami'an dake shirya gasar wasan cin kofin nahiyar Turai da za a yi a shekara mai zuwa a Faransa, sun ce ba za su amince da dage gasar ba daga yadda aka tsara.

Masu da'awar kafa daular musulunci sun ce sune suke da alhakin kai hari a kasar Faransa a ranar Juma'a da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 129 kuma 350 suka ji raunuka.

Jacques Lambert ya fada a wata kafar yada labarai a Faransa cewar da zarar sun dage gasar daga yadda aka tsara, abinda 'yan ta'adda suke so kenan.

Wannan shi ne karo na biyu da aka kai wa Faransa hari a cikin shekarannan, a inda a farkon Janairu aka kashe mutane 18 a gidan jaridar Charlie Hebdo yayin da aka kashe wani Bayahude da 'Yar sanda tana kan aiki a waje.

Mutane hudu ne suka mutu a lokacin da wani bam ya tashi daf da filin wasan kasar a lokacin da Faransa ke karawa da Jamus a wasan sada zumunci.

Faransa ce za ta karbi bakuncin wasannin gasar cin kofin nahiyar Turai da za a yi a filayen kasar da za a fara daga ranar 10 ga watan Yuni.