Amavi na Aston Villa ya gama buga Premier bana

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Amavi ya buga wa Aston Villa wasanni 12 a kakar wasan bana

Dan kwallon Aston Villa mai tsaron baya Jordan Amavi ya ji rauni a gwiwarsa, wanda zai yi jinya har zuwa karshen kakar Premier bana.

Dan wasan mai shekara 21, ya ji rauni ne a lokacin da yake buga wa tawagar Faransa 'yan kasa da shekara 21 wasa a karawar da suka ci Irelnad ta Arewa daya mai ban haushi a ranar Alahamis.

Amavi ya koma da taka-leda Aston Villa daga kulob din Nice na Faransa, kuma ya buga wasanni 12 a bana.

Aston Villa ce ta karshe a kan teburin Premier, amma ta buga canjaras da Manchester City a wasan farko da sabon kociya Remi Garde ya jagoranci kungiyar a wasan Premier.

Villa za ta buga wasan gaba na cin kofin Premier da Everton a ranar Asabar a filin wasa na Goodison Park.