Sunshine da Enyimba sun buga canjaras

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption Ranar Litinin za a karasa wasa tsakanin Warri Wolves da FC Taraba

Sunshine Stars ta buga wasa canjaras da Enyima a gasar cin kofin Firimiyar Nigeria wasannin mako na 38 da suka kara a jihar Legas, Nigeria.

Sunshine Stars ta karbi bakuncin Enyimba a Legas ne, sakamakon hana ta buga wasa a gida da hukumar gudanar da gasar ta hukunta kungiyar.

Tun a mako na 37 ne Enyimba ta lashe kofin bana a lokacin da ta hada maki 69 a mataki na daya a kan teburi, kuma kofi na bakwai da ta dauka jumulla.

Sunshine Stars kuwa ta kare a matsayi na shida ne a kan teburin da maki 61, yayin da Kano Pillars mai rike da kofin bara ta kammala a mataki na takwas da maki 55.

Kungiyoyi Hudu da ake sa ran za su yi ban kwana da gasar firimiyar Nigeria sun hada da Sharks da Kwara United da FC Taraba da kuma Bayelsa United.

Sai a ranar Litinin da safe za a cigaba da wasa tsakanin Warri Wolves da FC Taraba, sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya hana karasa karawar a ranar Lahadi.

Ga wasu sakamakon wasannin da aka buga a ranar Lahadi:

  • Sunshine Stars 0-0 Enyimba
  • Rangers 3-1 Bayelsa Utd
  • Kwara Utd 2-0 FC Ifeanyiubah
  • Heartland 2-1 El-Kanemi
  • Abia Warriors 1-0 Sharks
  • Akwa United 1-0 Lobi
  • Wikki 2-0 Kano Pillars