Fifa ta dakatar da Ganesh Thapa shakara 10

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An dakatar da Blatter daga shiga harkar kwallon kafa kwanaki 90

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, ta dakatar da wani mai fadi-a-ji a harkar kwallon kafar Asia, Ganesh Thapa, daga shiga harkokin kwallon kafa zuwa shekara 10.

An samu Thapa, mai shekaru 55, shugaban hukumar kwallon kafar Nepal kuma tsohon mataimakin shugaban hukumar kwallon Asia da laifin aikata ba daidai ba shekaru da dama.

Haka kuma hukumomin Nepal na bincikensa da yin almubazzaranci da miliyoyin kudaden da aka tara domin aikin bunkasa kwallon kafa.

Fifa ta kuma dakatar da shugaban hukumar kwallon kafar Lao, Viphet Sihachakr, daga shiga harkokin tamaula har tsawon shekara biyu.

Hukumar kwallon kafa ta duniya ta ce ta samu Sihachakr da laifin karbar na-goro bisa zaben kwamitin amintattun Fifa a taron nahiyar Asia a shekarar 2011.

Thapa, ya shaida wa BBC cewar zai kalubalnci hukuncin da hukumar kwallon kafar ta duniya, Fifa, ta dauka a kansa