Raul ya yi ritaya bayan shekara 21 yana kwallo

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Raul ya ci wa Real Madrid kwallaye 323, ya kuma bar kungiyar a shekarar 2010

Tsohon dan kwallon Real Madrid, Raul, ya yi ritaya daga buga tamaula bayan da ya yi shekara 21 yana taka-leda, inda ya lashe kofin gasar Amurka ta bana.

Raul ya taimaka wa New York Cosmos lashe gasar kudancin Amurka, inda suka ci Ottawa Fury 3-2.

Shi ne kuma wasan karshe da dan kwallon mai shekara 38, wanda ya dauki kofin La Liga shida da kofunan zakarun Turai uku ya buga kenan.

Raul ya bar taka-leda a Real Madrid a shekarar 2010, bayan shekara 16 da ya yi yana buga mata tamaula ya kuma ci mata kwallaye 323.

Tsohon dan kwallon Spaniya, ya kuma murza leda a Schalke ta Jamus da Al Sadd ta Qatar daga nan ya koma Amurka wasa.