An soke karawa tsakanin Belgium da Spaniya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ranar Talata ya kamata Belgium da Spaniya su kara a wasan sada zumunta

An soke wasan sada zumunta da aka tsara tsakanin Belgium da Faransa a ranar Talata, saboda dalilin tsaro, bisa harin da aka kai Faransa.

Mutane 129 ne suka mutu a harin da aka kai wa Faransa a ranar Juma'a, ciki har da harin da aka kai daf da filin da ake buga wasan sada zumunta da Faransa ke yi da Jamus.

Masu shigar da kara na Faransa sun gano dan kasar Belgium ne ya tsara harin ta'addacin da aka kai wa kasar.

Hukumar kwallon kafar Belgium ta ce ta soke karawar da aka tsara za su yi a filin wasa na King Baudouin tun farko bayan da ta tuntubi Spaniya.

A ranar Talata ce Ingila za ta karbi bakuncin tawagar Faransa a wasan sada zumunta da za su yi a Wembley.