Olsen ya ajiye aikin kociyan Denmark

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shekara 15 Morten Olsen ya ja ragamar Denmark

Morten Olsen ya yi ritaya daga horas da tawagar kwallon kafar Denmark, bayan da kasar ta kasa kai-wa gasar nahiyar Turai.

A ranar Talata ce Denmark ta tashi wasa 2-2 da Sweeden a was­an cike gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da suka yi.

A karawar farko da suka yi a ranar Asabar, Sweeden ce ta ci Denmark 2-1.

Olsen mai shekaru 66, tsohon dan kwallon Denmark ya horas da kasar wasannin tamaula har shekara 15.

Ya kuma fara aikin horas da tawagar ne bayan da aka kammala gasar cin kofin nahiyar Turai a shekarar 2000.

Faransa ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin nahiyar Turai da za a yi a shekarar 2016.