ATP World Tour: Federer ya doke Kei

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Federer dai ya kawo karshen mafarkin da Kei na samun nasara a wanna matakin.

Roger Federer ya ci gaba da rike matsayinsa na zakara a gasar ATP World Tour bayan da ya yi galaba kan Kei Nishikori a wasan karshe na rukuninsu da suka buka dazu a London.

Federer dai ya samu galaba ne da maki 7 da 5 a zagayen farko, aka doke shi da maki 4 da 6 a zagaye na biyu, sai kuma ya yi galaba da maki 6 da 4 a zageye na uku a filin wasa na O2 Arena.

A yanzu dai Federer zai kara a wasan gab da karshe ne da ko dai Novak Djokovic ko kuma Tomas Berdych.

Djokovic dai na bukatar yin nasara a zagaye guda kawai kan Berdych a yayin karawar da za su buga da daren ranar Alhamis, domin neman kai wa ga wannan matakin.

Karin bayani