A shirye nake na tunkari Barca — Gareth Bale

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gareth Bale ya ce ya shirya tunkarar Barcelona a filin El-Clasico.

Dan wasan gaba na Real Madrid Gareth Bale ya ce a shirye yake ya tunkari abokan hamayyarsu Barcelona a fafatawar da za su yi ranar Asabar a gasar El Clasico.

Bale, dan asalin Wales mai shekaru 26, ya ji rauni a watan Oktoba, kuma hakan ya sanya shi dakatar da wasanni hudu.

Ya ce, "Na yi jinyar kusan makwanni shida, bayan haka ban samu damar buga wasanni a wannan kakar ba. Amma ina jin karfin jiki na yanzu, kuma na shirya wa wannan wasan".

Bale bai buga a wasan sada zumunta da Wales ta sha kaye a hannun Netherlands da ci 3-2 ba.

Kulob din Barcelona, wanda shi ne ke kan gaba a gasar El Clasico, yana wuce Real Madrid da maki uku, kuma Lionel Messi zai buga wasan bayan shi ma ya dawo daga jinyar da ya yi a watan Satumba.